Chibok: dalibai 4000 sun yi gangami a Philippines

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kasashe da dama sun yi gangami game da sakin 'yan matan na chibok

Kimanin dalibai 4000 na makarantar mata ta cocin Roman Katolika sun yi gangami a kasar Philippines, domin neman a sako 'yan matan Chibok.

Daliban sun bi sahun al'ummar duniya da ke fafutukar ganin an sako 'yan mata 'yan makaranta fiye da 200 da kungiyar Boko Haram ta sace a Najeriya.

Masu gangamin a Manila baban birnin kasar, sun yi ta furta kalaman cewa "A sako su" inda kuma suka bukaci masu motoci su yi ta danna ham din motarsu, domin nuna goyon baya.

Fiye da watanni biyu kenan da sace 'yan matan a Nigeria, kuma kawo yanzu babu duriyarsu.