Jonathan ya ziyarci wurin harin Abuja

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A ranar Alhamis ne shugaban ya katse halartar taron kungiyar Afrika a Malabo ya dawo gida saboda harin

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya ziyarci wurin da aka kai harin bam da ke rukunin shaguna na Emab a Wuse II a birnin Abuja.

Mr. Jonathan wanda ya kai ziyarar cikin tsauraran matakan tsaro ya yi tur da harin da kuma wadanda ya kira makiya ci gaban kasa.

Haka kuma shugaban ya kai ziyara babban asibitin Maitama, inda ake kula da wadanda suka jikkata a harin, ya kuma jaddada cewa gwamnatin za ta yi duk abin da za ta iya domin kawo karshen ta'addanci a kasar.

Ya kuma shaida wa majinyatan cewa gwamnati za ta dauki nauyin kula da su da na magunguna da kuma abincinsu.