'Yan sanda sun kwance bam a Kano

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rundunar 'yan sandar ta ce bama-baman na da hadari

Rundunar 'yan sandan jihar Kano a arewacin Nigeria ta ce jami'an ta sun kwance wasu manyan bama-bamai da aka gano a Unguwar Sauna Kafinga dake karamar hukumar Nasarawa a birnin.

Rundunar ta ce an ajiye bama-baman ne a cikin wata mota kusa da Masallacin Juma'ar yankin, kuma an gano su ne da misalin karfe 1:30 na ranar Juma'a, yayin da wasu suka sanar da rundunar.

Bama-baman sun kai 13 wadan da suke da hadarin gaske.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Alhaji Aderinle Sinaba ya shaidawa wani taron manema labarai a jihar cewar bama-bama na da matukar hadari

An kuma samu bindiga daya da harsasai a cikin motar.

A ranar Litinin din da ta gabata ne dai wani bam ya tashi a makarantar koyan aikin duba gari a jihar, wanda ya janyo mutuwar kusan mutane takwas.

Karin bayani