'Sojoji sun yi gwajin makamai a Maiduguri'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jihar Borno wadda ita ce tungar Boko Haram ya kasance a karkashin dokar ta-baci

Wani dan kato da gora ya shaida wa BBC cewa sojoji sun ce sune suka gwada makamansu a wajen Maiduguri.

A cewarsa hakan ya biyo bayan bayanan sirin da sojoji suka samu na cewa 'yan kungiyar Boko haram za su shiga Maiduguri domin su yi azumi a can.

Rahotannin farko dai sun ce mazauna birnin sun ji karar fashewar wasu abubuwa da kuma harbe-harben bindiga a wajen birnin, lamarin da ya jefa su cikin zullumi.

Karar harbe-harben dai ya sa wasu sun kwana a kan tituna, sai dai mazauna birnin sun ce a yanzu komai ya lafa.