Norway ta kawo karshen kuriar yanar gizo

Image caption Norway ta dakatar da amfani da zabe ta hanyar yanar gizo

Kasar Norway ta kawo karshen gwajin amfani da naura mai kwakwalwa wajan zaben kasa da na kananan hukumomi.

Gwaje gwajen da akayi na kada kuri'a ta hanyar yanar gizo anyi su ne a zabukan da aka yi a shekara ta 2011 da kuma 2013.

Amma gwamnatin ta ce wannan gwajin ya zo karshe ne saboda tsoron da masu kada kuri'ar suka nuna cewa zabensu na zama a bainar jama'a.

Masu kada kuri'ar sun yi ikirarin cewa irin wannan zaben ka iya kawo cikas ga dimokradiyya.

Hakkin mallakar hoto Bhaskar Solanki
Image caption Norway ta dakatar da zaben Yanar gizo

Rikicin siyasa da kuma la'akari da cewa gwajin bai kara fitowar masu kada kuri'a ba ya dada sawa an kawo karshen gwajin.

A wata kuma sanarwa daga ofishin dake kula da harkokin zamani na kasar Norway ya ce an kawo karshen gwajin ne saboda muhawara da akayi a Majalisar Kasar kan yunkurinsu na kawo sauyi a tsarin gudanar da zabe.

Wani kuma rahoto da ke duba nasarar da gwajin ya samu a shekara ta 2013 na cewa kusan 'yan kasar Norway dubu saba'in sun kada kuri'a ta hanyar yanar gizo.

Sai dai rahoton ya ce babu wata shaida da take nuni cewa gwajin ya kara yawan wadanda suka kada kuri'a ko kuma ma ya sa wasu rukunin mutane da basu taba zabe ba suka yi zabe.

Karin bayani