Chibok: anyi zanga-zanga a Lagos

Jama'a dadama ne suka yi gangami dazu a birnin Lagos, don matsawa gwamnatin kasar lamba akan ta kubutar da 'yan matan Chibok da aka sace.

Yanzu wata biyu da rabi kenan tun bayan da kungiyar Boko Haram ta sace 'yan mata su fiye da dari biyu, daga garin Chibok na jahar Borno.

Kuma har yanzu ba'a san inda suke ba.

Ana cigaba da matsa wa gwamnatin Najeriya lamba, a ciki da wajen kasar, na ta kara hobbasa don ceto 'yan matan.

Wasu daruruwan mata a Lagos sun gudanar da zanga-zangar lumana, suna neman gwamnatin ta yi wani abu game da lamarin.

Daya daga cikin masu zanga-zangar ya shaidawa BBC cewa "gwamnati ba da gaske take ba wajen gano 'yan matan da aka sace ba."

Sai dai gwamnatin Najeriya tace tana iya kokarinta wajen kubutar da daliban.

Tun a watan Afrilu ne aka sace 'yan matan daga dakin kwanan su a makarantar sakarinden Chibok din.