Kuri'ar raba gardama a Hong Kong

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hukumomi a Hong Kong basu amince da zaben ba

Masu zabe a Hong Kong na kada kuri'a a rana ta karshe ta zaben raba gardama, wanda ba na hukuma ba, wanda kuma sakamonsa ba zai shafi sauye sauyen dumokradiyya ba.

Kawo yanzu sama da mutane dubu 700 , kashi daya bisa biyar ne, na masu zaben suka kada kuri'a, ko dai ta intanet ko kai tsaye , a kwanaki tara da aka yi ana zaben.

Mazauna Hong Kong din dai suna samun 'yanci da walwala da babu su, a sauran sassan China, amma kuma hukumomin Chinan sun ayyana zaben raba gardamar a matsayin haramtacce.

Wakilin BBC a Hong Kong ya ce rashin amincewar hukuma kan zaben ya sa mutane da dama sun kaurace masa.