Dakarun Iraqi sun ce sun kwace Tikrit

Dakarun Iraqi Hakkin mallakar hoto Reuters

Gidan talabijin din gwamnatin Iraki ya bada rahoton cewa, sojojin gwamnatin sun sake kwato birnin Tikrit na arewacin kasar, daga masu fafutuka 'yan Sunni.

'Yan tawayen sun karbe iko da shi ne fiye da makonni biyu da suka wuce.

Rahoton ya ce, an kori dukan mayakan kungiyar Islama ta ISIS daga Tikrit din, kuma an hallaka 'yan gwagwarmayar sittin, ciki har da kwamandojinsu.

To sai dai masu magana da yawun 'yan tawayen sun karyata labarin.

Sun tabbatar cewa, lallai sun yi gumurzu da dakarun gwamnati a kewayen birnin na Tikrit, amma kuma a yanzu suna cigaba da fatattakar sojojin da suka rage.

A daya bangaren kuma, majiyoyin asibiti dana soji sun ce an hallaka akalla dakarun gwamnatin kasar ashirin a wani kastamin gumurzu a kudancin Gadaza.