Iraqi ta yi odar jiragen yaki daga Rasha

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Nan da 'yan kawanaki za a fara amfani da jiragen guda biyar domin yakar 'yan tawaye

Iraqi ta ce ta karbi kashin farko na kwancen jiragen yakin da ta saya daga Rasha, domin yakar 'yan tawayen Sunni da suka kwace yankunan kasar da dama.

Ma'aikatar tsaron kasar ta ce nan da 'yan kawanaki za a fara amfani da jiragen guda biyar, kuma akwai saura da ke kan hanya.

A ranar jiya Asabar gwamantin Iraqin ta ce, dakarunta sun sake kwato birnin Tikrit, a wani gagarumin farmaki da suka kai wa mayakan na kungiyar ISIS, kuma suna shirin durfafar Mosul.

'yan tawayen dai sun tabbatar da aukuwar gumurzun na Tikrit, amma kuma , sun nuna cewa farmakin bai yi nasara ba.