'Ba mu hana tashi zuwa aikin Umrah ba'

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Sojoji sun ce sun takaita amfani da filin jirgin Maiduguri saboda tsaro

Hedikwatar Tsaron Nigeria ta bayyana cewa an takaita zirga zirgar amfani da filin jirgin saman Maiduguri ne zuwa ayyukan soji, sakamakon irin aikace aikacen da sojojin suke yi na tabbatar da tsaro a yankin.

Sanarwar mai dauke da sa hannun Manjo Janar Chris Olukolade ta musanta rahotannin da kafofin yada labaru suka bayar da ke cewa an rufe filin jirgin saman ne domin hana maniyyata aikin Umrah tashi.

Sanarwar ta ce an dauki matakin ne sakamakon yanayin tsaro da akai la'akari da shi, wanda ke nuna cewa ba za a iya jigilar tarin mutane daga filin jirgin ba, sakamakon barazanar tsaro da ake fuskanta da kuma ayyukan tabbatar da tsaro da ake yi a yankin.

Sanarwar ta kara da cewa ga alamu wadanda suka shirya jigilar ba su ankara da irin hadarin da ke tattare da amfani da wannan filin jirgin ba a yanayin da ake ciki.

Sai dai sanarwar hedikwatar tsaron Najeriyar ta ce suna kokarin samar da wata hanyar da za ta tabbatar da aikin jigilar.

Daga karshe sanarwar ta umarci jama'a suyi watsi da yi wa wannan al'amari fassara da ta danganci addini ko kuma siyasa.