Bam ya tashi a garin Bauchi

Jihar Bauchi a Najeriya
Image caption Jihar Bauchi a Najeriya

'Yan sanda a Najeriya sun ce mutane goma sha daya ne aka kashe yayin da 34 suka ji raunuka sakamakon fashewar bam a cikin garin Bauchi a daren jiya.

Bayanai sun ce bam din ya fashe ne a gidan mata masu zaman kansu .

Sai dai kawo yanzu babu wani da ya dau alhakin kai harin, sai dai a baya kungiyar boko haram ta kai hare hare a Bauchi.

Mutane akalla ashirin da daya ne suka hallaka lokacin da bam ya tashi a wani rukunin shaguna a birnin Abuja , ranar larabar da ta gabata , kuma ana zargin kungiyar boko haran da kai harin.