Musulmi sun fara a azumi a Najeriya

Image caption Musulmai a Najeriya za su dauki azumin watan Ramadan

Jama'r Musulmi dadama sun tashi da azumin Ramadan a Najeriya bayan da aka bada sanarwar ganin watan.

Sai dai akwai wasu da basu tashi da azumin saboda a cewar su basuji sanarwar da akayi a daren jiya ba.

Fadar Sarkin Musulmi na Najeriya, Alhaji Sa'ad Abubakar na ukku ne ta ba da sanarwar.

An ce anga watan ne a Sakwkwato da Argungu da Jigawa da kuma Gwandu.

Wasu musulmi a garin Dutse, babban birnin jihar Jigawa, sun shaidawa wakilin BBC cewa su basu tashi da azumin bane saboda basuji sanarwa ba.

Tun farko dai an bada sanarwwar cewa ranar lahadi ne ake saran fara azumin na bana.

Watan Ramadan wata ne mai girma a addinin Musulunci inda Musulami ke neman gafara da neman yardar Allah Ubangiji Madaukakin Sarki.

Karin bayani