Norway: zabe ta Intanet bai yi tasiri ba

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Zaben ta Intanet a Norway bai karfafa wa wasu guiwa ba

Wani rahoto ya nuna cewa ba a samu karuwar masu zabe ba, a zaben da aka gudanar a Norway na gwaji ta hanyar amfani da intanet.

An gudanar da gwajin zaben ne ta hanyar amfani da kwamfuta a zabukan kasa da kuma na kananan hukumomi a 2011 da 2013.

An kawo karshen gwajin ne saboda, kamar yadda gwamnati ta ce, fargabar da masu zabe ke nunawa cewa za a iya sanin abin da suka zaba, ta sa wasu ba su yi zaben ba.

A wata sanarwa da ofishin kawo sauye-sauye na zamani na Norway, ya fitar, ya ce, an dakatar da shirin ne sakamakon tattaunawar da aka yi a majalisar dokokin kasar ta neman inganta tsarin.

Sanarwar ta ce duk da cewa akwai burin barin mutane su yi zabe ta intanet, mummunan sakamakon da aka samu a gwaji biyu da aka yi na baya , ya sa gwamnati ta dakatar da kashe kudi a kan shirin.

Image caption zabe ta intanet

Binciken da aka yi kan nasarar gwajin shirin a 2013 ya nuna cewa kusan 'yan Norway dubu 70 ne suka yi zaben ta intanet.

Kuma wannan shi ne kashi 38 cikin dari na duka masu zabe 250,000 a garuruwa da birane 12 na wadanda za su iya zaben ta intanet.

Hakan kuma ya nuna cewa ba bu wata sheda da ta tabbatar da karuwar masu zabe sanadiyyar amfani da intanet din.

Rahoton ya kuma nuna cewa, wani dan kashi na masu zaben da bai kai daya cikin dari ba, ya yi zabe sau biyu a 2013.

Ya ce sun yi hakan ne kuwa ta hanyar kada kuri'arsu ta farko ta inatnet, sannan kuma suka je rumfar zabe suka yi zabe na takarda.