Birtaniya na fuskantar karancin filayen noma

Hakkin mallakar hoto Getty

Wani sabon bincike ya nuna cewa Birtaniya na fuskantar karancin filin noma kuma tana fuskantar karancin hekta miliyan 2 zuwa shekarar 2030

Rahotan daga jami'ar Cambridge ya ce karuwar al'umma da kuma amfani da fili wajen noma amfanin gona dake samar da makamashi ya taimaka wajen hakan.

Rahotan ya soki gwamnatin Birtaniya saboda rashin tsari na yadda zata yi amfani da filayen noman kasar ta hanyar da ta dace

Masu wallafa rahotan sun yi gargadin cewa dole ne nan gaba ana bukatar zabi masu tsauri domin amfani da gonaki

Girman filin kasar dai ya haura hekta miliyan 24 kuma ana amfani da fiye da kashi 75 cikin 100 wajen noma

Yayinda kasar ke da wadatar kayayyaki irinsu alkalama da madara sai dai kuma tana shigo da kayan itatuwa da ganyayyaki da kuma naman alade

Yayinda ake tsammanin al'ummar kasar zasu zarta mutane miliyan 70 zuwa shekarar 2030, bukatar da za'a samu ta karin wajen zama da kuma abinci zai yi babban tasiri akan yadda ake amfani da fili kamar yadda rahotan ya ce