'Yan bindiga sun kai hari kusa da Chibok

Makarantar da aka sace 'yan mata fiye da 200 a Chibok Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A garin Chibok ne aka sace dalibai fiye da 200 daga makarantar sakandaren 'yan mata

A Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, wadansu 'yan bindiga da ake kyautata zaton cewa 'yan Boko Haram ne sun kai hari a kan wadansu garuruwa hudu a kusa da Chibok.

Wani dan banga a daya daga cikin garuruwan ya shaida wa BBC cewa an kai harin ne a kan garuruwan Kautikari, da Nasarawa, da Gwaradina, da kuma Kwadake, inda mutane da dama suka rasa rayukansu.

Ya kuma ce an tura wani jirgin saman yaki don ya fatattaki masu kai harin, amma bai isa wurin a kan lokaci ba.

Dan Majalisar Dattawan Najeriya mai wakiltar Kudancin Borno, Mohammed Ali Ndume, da dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Askira-Uba, Peter Biye, sun ce suna da labarin kai harin, amma ba su da hakikanin alkaluman mutanen da abin ya shafa.

Hukumomin tsaro na kasar dai ba su ce komai ba tukunna a kan lamarin.

Yankin dai na ci gaba da fuskantar hare-haren da ake alakantawa da masu ta-da-kayar baya na kungiyar Boko Haram duk kuwa da dokar ta-bacin da gwamnatin Najeriyar ta ayyana fiye da shekara guda da ta gabata.

Karin bayani