Gini ya rufta da jama'a a India

Gini ya rushe a India Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gini ya rushe a India

Jami'ai a India sun ce akalla mutane 11 sun rasa rayukansu, lokacin da wani ginin da ba a kammala ba ya rufta a jahar Tamil Nadu.

An yi amunnar cewa galibin wadanda suka mutun leburori ne da ke aikin ginin mai hawa goma sha biyu.

Ana jin akwai wasu mutanen dayawa da ginin ya danne.

Jami'i mai kula da kai daukin gaggawa a yankin ya ce, dole sai sun kwashe buraguzan ginin tukuna, kafin su iya kaiwa ga wadanda suka tsira.

Ya ce wannan shine abun da suke ba fifiko a yanzu.

Kafofin yada labarai a yankin sun ce ana ruwan sama kamar da bakin kwarya a lokacin da ginin ya ruguje.

'Yan sanda sun kama darektoci biyu na kamfanin da ke ginin.