Sojojin Iraki na luguden wuta a Tikrit

Farmakin sojan Iraki a Tikrit Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Farmakin sojan Iraki a Tikrit

Rahotanni sun ce sojojin gwamnatin Iraki sun cigaba da yin barin wuta a birnin Tikrit, kwana daya bayan sun fuskanci koma baya daga mayakan Sunni a yunkurin farko da suka yi.

Yawancin sojojin Irakin sun janye daga birnin bayan an kashe dayawa daga cikinsu a artabun da aka yi a jiya.

An ce ana cigaba da yin artabu a lardin Qadissiyah da ke arewa.

A cewar wasu majiyoyi, dakarun tsaron Irakin na fuskantar kalubale wajen kaiwa tsakiyar garin na Tikrit, saboda mayakan na kungiyar ISIS sun baza bama-bamai a kan babbar hanyar da ake bi.

Wani wakilin BBC ya ce kusan ba kowa a birnin na Tikrit, saboda yawancin mutane sun tsere kafin murtanin da sojojin gwamnati suka mayar.