Za a ci gaba da yi wa Pistorius shari'a

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Pistorius ya harbe budurwar tasa ne da daren ranar masoya ta Valentine.

Ana saran a ci gaba da shari'ar da ake yi wa dan tseren Afirka ta Kudun nan Oscar Pistoriuos a Pretoria ranar Litinin, bayan hutun makonni shidan da aka tafi yayinda kwararru ke bincikar lafiyar kwakwalwarsa.

Lauyoyin da e kare shi, sun ce yana fama da matsalar damuwa ne a lokacin da ya kashe buduwar tasa Reeva Steenkamp a cikin gidansa a bara.

Gwajin da za a yi masa na hankali ka iya nuna ko Mr. Pistoriuos ne ke da alhakin kisan nata ko kuma a'a.

Dan wasan tseren dai ya kafe cewa ya dauke tane a matsayin wanda yai kutse cikin gidansa.

Karin bayani