Ban ya yi tir da hare-hare a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan bindigar da ake zargin 'yan boko haram ne sun zafafa hare haren su a Borno

Sakatare Janar na majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon, ya yi Allah wadai da hare-haren da ake kaiwa a wasu sassan Najeriya musamman a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

Ban Ki moon ya ce ci gaba da kai hare-haren kusan a kullum abin kaicho ne, kuma a shirye majalisar dinkin duniyar ta ke ta taimaka wa Najeriya don kawo karshen hare-haren.

Sakatare Janar na majalisar dinkin duniyar ya yi wadannan kalaman ne sakamakon hare-haren da aka kai kan wasu kauyuka da ke kusa da Chibok na jihar Borno a karshen mako, inda aka kashe mutane da dama.

Mazauna kauyukan da aka kaiwa hare-haren dai, sun koka a kan cewa sun nemi daukin jami'an tsaro, amma ba su taimaka musu ba.

Sai dai Mista Mike Omeri, darakatan cibiyar samar da bayanai kan 'yan matan Chibok, ya ce dakarun tsaro suna iyakar kokarinsu.