Kamaru na samar da tsaro a wuraren ibada

Jami'an tsaro a Kamaru Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu na zargin jami'an tsaro a Kamaru da afka wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Gwamnatin Kamaru na tsaurara matakan tsaro a masallatai da coci-coci da ke sassa daban daban na kasar.

Haka kuma gwamnatin na sa ido kan irin wa'azin da malaman addinin Musulunci ke yi a masallatai musamman a lardin arewa mai nisa da kuma yankin kudancin kasar yayin da aka fara azumin watan Ramadan.

Gwamnatin dai na daukar wannan mataki ne don kaucewa yada tsatsaurar akidar 'yan kungiyar Boko Haram a kokarin da ta ke yi na tarwatsa sansanonin 'yan kungiyar a yankin arewacin kasar.

Sai dai yayin da hukumomin ke kara tsaurara matakan tsaro, al'ummar Musulmai a duk fadin kasar sun gudanar da wani gangami na kasa baki-daya inda su ka nisanta kansu da kungiyar ta Boko Haram.