Binciken halayya: Facebook na fuskantar suka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An yi binciken akan masu amfani da facebook kusan mutane 700,000

Facebook na fuskantar suka bayan da ta bayyana cewa ya aiwatar da gwaji kan halayyar masu amfani da shafin kusan mutane 700,000.

Kuma Facebook ya gudanar da wannan gwaji ne ba tare da sanin mutanen ba

An gudanar da wannan bincike ne tare da hadin gwiwar wasu jami'oin Amurka biyu domin auna ko yadda mutum ke ji a ransa zai iya sa ya canza irin bayanan da zai sanya a shafin

Sai dai Facebook ya ce babu daya daga cikin bayanan da akai amfani da shi a gwajin da ya dace da wani mutum

Jami'oin Cornell da kuma Jami'ar California a San Francisco na cikin wannan bincike

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasu sun bukaci a gudanar da bincike game da wannan batu

Amma wasu sun soki hanyar da aka bi wajen gudanar da binciken.

Irin wadannan masu suka sun kuma nuna damuwa game da irin tasirin da binciken zai yi

Lauren Weinstein ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa Facebook ya gudanar da gwaji akan masu amfani da shafinsa cikin sirri domin kokarin bakanta musu.

Shima wani dan majalisar dokoki na jam'iyyar Labour Jim Sheridan ya yi kira da a gudanar da bincike cikin wannan al'amari