Israila ta gano gawarwakin matasa uku

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Matasan Isra'ila da aka kashe

Jami'an tsaron Isra'ila sun ce sun gano gagawakin wasu matasa uku da suka bace a lokacin da suke kokarin direbobin motoci su rage ma su hanya kyauta a Gabar Yammacin kogin Jordan a farkon wannan watan.

Wani kakakin rundunar sojin Isra'ilar ya ce an gano gawawakin ne a karkashin wasu duwatsu a wata gona dake kusa da birnin Hebron na Gabar Yammacin Kogin Jordan.

Wakiliyar BBC ta ce tun farko gidan talabijin na Isra'ila ya nuna sojojin Isr'ailar da dama da aka tura garin Palasdinawa na Halhul, kusa da inda aka yiwa matasan gani na karshe.

A halin da ake ciki kuma, Pira ministan Isra'ilar , Benjamin Netanyahu ya kira wani taron gaggawa na majalisar ministocin tsaron kasar.

Isra'ila ta zargi kungiyar Palasdinawa ta Hamas da hannu a sace matasan, amma Hamas din ta musanta zargin.

Karin bayani