Ba tsaro a wasu Tashoshin motocin safa a Abuja

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane da dama sun mutu a harin da aka kai kan tashar mota dake Nyanya

A Najeriya, tun lokacin da kungiyar da ake cewa boko haram ta kai hari kan wata tashar mota dake unguwar Nyanya a Abuja, mahukunta a kasar ke ikirarin inganta tsaro a musamman tasoshin mota da sauran wuraren dake hada jama'a.

Ana dai gudanar binciken fasanjojin dake shiga mota ne don tabbatar da cewa masu aikata laifi basu samu damar shiga gari ko tsakanin jama'a da abubuwan da zasu cutar da su ba.

Sai da binciken da BBC ta gudanar a tashar motocin safa dake kusa da gadar Nyanya, ya nuna cewa babu wani bincike irin na tsaro da ake yi wa fasinjoji.

Wasu fasinjoji sun shaidawa BBC cewa kowa yana shiga cikin motocin safa safa ne ba tare da an bincike shi ba.

Irin wadannan fasinjojin sun bayyana damuwa da kuma fargabarsu.

Sai dai Shugaban cibiyar da ke samar da bayanai akan harkar samar da tsaro a Nigeria Mr Mike Omere ya shaidawa BBC cewa zasu gudanar da wata mahawara da Shugabannin kungiyoyin masu motocin safa safa domin ankarar da su kan mahimmancin daukar matakan tsaro a wuraren shiga motocin.