Za a ci gaba da shari'ar Oscar Pistorius

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An yiwa Pistorius gwajin lafiya

Yau ake saran cigaba da shari'ar da ake yiwa dan tseren Afirka ta Kudun nan Oscar Pistoriuos a Pretoria, bayan hutun makonni shidan da aka tafi, yayinda kwararru ke bincikar lafiyar kwakwalwarsa.

Lauyoyin dake kare shi, sun ce yana fama da matsalar damuwa ne a lokacin da ya kashe buduwar tasa Reeva Steenkamp a cikin gidansa a bara.

Gwajin da za'a yi masa na hankali , ka iya nuna ko Mr Pistoriuos nada alhakin kisan budurwar tasa ko kuma a'a.

Dan wasan tseren dai ya kafe cewa ya dauke tane a matsayin wanda yai kutse cikin gidansa