Za a jibge tulin makaman syria masu guba

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Za a lalata makaman a yankin Mediterranean

An kara tsaurara matakan tsaro a kudancin tashar jiragen ruwan Italiya ta Gioia Tauro inda nanne za a kai tulin makaman syria masu guba a wannan makon.

Watanni bayan da kasashen duniya suka amince da wa'adin da aka deba tun farko, an karkafa wuraren duba ababen hawa, sannan za a hana jirage tashi a wani yanki mai nisan kilomita guda.

Wani jirgin ruwan kasar Denmark zai isa wajen makare da kwantenoni dake cike da abubuwan da Spetocin majalisar dinkin duniya suka ce dasu ne ake harhada makamai masu guba a doran kasa.

Daga nan za a juye Kwantenonin zuwa wani jirgin ruwan Amurka, wanda zai lalata su a wani wajen da ba'a bayyana ba, a yankin Mediterranean.