Faransa za ta dauki mataki kan masu tafiya jihadi

Dan gwagwarmayar kungiyar ISIS Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dan gwagwarmayar kungiyar ISIS

Faransa za ta gabatar da sababbin matakan hana yan kasarta bin sahun yan gwagwarmayar Musulunci a Syria da Iraqi.

Wata sabuwar doka da majalisar ministoci ta amince da ita za ta bayar da dama ga hukumomi su hana mutane daga yin tafiya, idan sun zargi suna da wata alaka da kungiyoyin masu tsatstsauran ra'ayi.

Faransa ta ce matasa musulmi daga 2 zuwa 3 ne ke tafiya a duk rana, suna tashi zuwa Turkiya ta jirgin sama kafin su ketara kan iyaka su shiga cikin masu Jahadi.

Ana dai kara jin tsoro a Faransa da sauran kasashen Turai cewar za su dawo daga fada a gabas ta tsakiya su kaddamar da hare hare a Turai.

Ministan cikin gida na Faransa Benart Cazeneuve ya shaidawa BBC cewa akwai karuwar faragaba a Faransa da sauran kasashen duniya, kan cewa matasan za su dawo kasashensu da tsattsauran ra'ayi tare da kaddamar da hare-hare