Najeriya ce kan gaba a noman tabar Wiwi

Ganyen tabar wiwi Hakkin mallakar hoto cannabis
Image caption Ganyen tabar wiwi

Hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta duniya ta ce Najeriya ce tafi kowace kasa yawan noma ganyen wiwi a Africa.

Hukumar ta bayyana hakan a yayin gabatar da rahoton ta a gaban hukumomin yaki da miyagun kwayoyi da magunguna da abinci a Najeriya.

Kasar Masar ita ce ke biye da Najeriya.

Rahoton ya ce ganyen tabar wiwi yana da saurin samu ga jama'a kwatankwacin miyagun kwayoyi irinsu Amphatemine a yankin Asiya da kuma hodar Cocaine a Amurka.

Wakiliyar hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta majalisar dinkin duniya, Maryam Sisoko ta ce a wannan shekarar rahoton ya nuna kimanin mutane miliyan 243 wadanda shekarunsu suka kama daga 15 zuwa 64 ne ke amfanin da miyagun kwayoyin da aka haramta.

Sai dai Shugaban hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta Najeriya -NDLEA, Alhaji Amadu Giyade, ya ce ganyen wiwi ne kawai ake nomawa a Nijeriya.