Za a rufe filin jirgin sama na Abuja

Jirgin sama da ke shirin ta shi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bangaren sufurin jiragen sama a Nigeria na fuskantar kalubale da dama

Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Nigeria ta ce za ta rufe hanyar da jiragen sama ke sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Hukumar ta ce za ta yi hakan ne don gudanar da gyare-gyare a hanyar saukar jiragen sama a filin a ranakun Asabar da Lahadi.

Rahotanni sun ce rufe filin jirgin saman ka iya janyo tsaiko a harkar zirga-zirgar jiragen sama a Abuja.

Harkar sufurin jiragen sama a Nigeria na fuskantar kalubale da dama wadanda suka hada da rashin ingantattun kayayyaki na zamani a filayen jiragen sama da ke kasar.