'Shettima na zargin 'yan siyasa a Borno'

Hakkin mallakar hoto
Image caption Hare hare na karuwa a jahar Borno a baya bayan nan

Gwamnatin Jihar Borno da ke arewacin Nigeria ta yi gargadin cewa akwai wasu 'yan siyasa da ke yi mata makarkashiya a yunkurin da take na magance matsalolin tsaro.

Hakan na zuwa ne daidai lokacin da hare-haren 'yan bindiga a Jihar Bornon ke karuwa a 'yan kwanakin nan.

A wata sanarwa da ta bayar, gwamnatin jihar Bornon ta ce mutanen dake wannan makarkashiya suna kokarin gwara kan gwamnatin Tarayya ne da Sojoji da kuma gwamnatin jihar Bornon, don kada su fahimci juna.

Sanarwar ta kara da cewa burin wadannan mutane baya wuce siyasa, yayinda ake tunkarar zaben shekara ta 2015.

Gwamnatin Bornon dai ta ki amincewa da cewa tamkar tana rufa-rufa ne kawai saboda zargin da wasu ke yi cewar an kasa magance matsalar tabarbarewar harkar tsaro ne a cikin Jahar.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar dubban mutane a Nigeria tun daga shekara ta 2010.

Karin bayani