'Haramta sanya gilashin google a gidajen cinema a Birtaniya'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gilashin google yana nadar bidiyo

Shugaban kungiyar masu nuna fina finai ta gidajen cinema a Birtaniya ya bukaci a haramta amfani da gilashin ido na Google a gidajen cinema na kasar

Phil Clap ya ce yana son a daina sanya gilashin imma ana yin fim ko kuma a'a

Kungiyar dai bata da hurumin tilasta haramcin, amma a madadin haka tana bada shawara ne ga mafiyawancin gidajen cinema na Kasar

Google dai ya bukaci gidajen cinema su nemi masu sanya gilashin da su kashe shi kafin a soma fim

A wata sanarwa kamfanin ya ce ya kamata a dauki gilashin Google, wanda ka iya nadar bidiyo tamkar na'urori irinsu wayoyin salula

Hakkin mallakar hoto
Image caption An kaddamar da gilashin Google a Birtaniya a makon da ya gabata

Kungiyar masu nuna fina finai ta gidajen cinema na wakiltar kusan kashi casa'in cikin dari na gidajen cinema a Birtaniya

Kungiyar tana kuma kare muradun kungiyoyi irinsu hukumar yaki da satar hakkin mallaka

An dai ambato Babban jami'in kungiyar Phil Clapp yana cewa za'a bukaci kwastomomi da kada su sanya wadanan gilasan a cikin dakunan Cinema

Gidajen cinema dai suna da 'yancin su yanke shawara akan wannan batu

An kaddamar da gilashin Google a Birtaniya a makon da ya gabata amma ba'a tsammanin zai zama ruwan dare saboda farashin da aka sanya masa.