An yi jana'izar matasan Israila da aka kashe

Taron jana'iazar matasan Israila da aka gano gawarwakinsu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Taron jana'iazar matasan Israila da aka gano gawarwakinsu

.Dubban yan Isra'ila ne suka halarci jana'izar matasan nan 3 da aka gano gawarsu a yankin yammacin kogin Jordan da ke mamaye a jiya litinin.

Bayan jawabai daga shugaban Isra'ila da kuma Pirayim Minista, an bizne matasan 3 jere da juna a wata jana'iza ta musamman.

Gwamnatin Isra'ila dai ta dora alhakin kisan nasu a kan kungiyar yan gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas kuma ta yi alkawarin daukar fansa.

Matasan sun bace ne fiye da makonni 12 da suka wuce yayin da suke neman a rage masu hanya a yankin gabar yamma ta kogin Jordan.

Hamas ta musanta kasancewa da duk wani hannu a kisan.

Isra Almodallal ta ofishin watsa labarai na hukumar Palasdinawa ta ce Palasdinawa ba sa da alaka da bacewar matasan

Karin bayani