Bam ya fashe a Asikolaiye dake Kaduna

A jihar Kaduna da ke arewacin Nigeria wani abu da ake zaton bam ne ya fashe a Asikolaiye da ke kusa da babban titin Nnamdi Azikwe.

Lamarin ya faru ne jim kadan bayan an shan ruwa a yau dinnan.

Rahotanni sun ce bam din ya fashe ne tsakanin masallacin Sheikh Dahiru Usman Bauchi da kuma hanyar zuwa gidansa.

Ba a sami rahoton hasarar rayuka ko kuma jikkata ba. Sai dai an ce bam din girgiza gidaje a kusa da inda ya fashe.

Karin bayani