Stephen Keshi ya yi murabus

Stephen Keshi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Stephen Keshi

Kociyan Nigeria, Stephen Keshi ya yi murabus bayan da aka yi waje da Nigeria daga wasan cin kofin duniya a Brazil.

Nigeria ta sha kashi ne a hannun Faransa da ci 2 ba ko daya.

Kasar Faransar ta ci Nigeria kwallo biyu ne a cikin mintina 11 na karshe.

An nada Stephen Keshi, mai shekaru 52 da haihuwa ne a matsayin kocin Nigeria a shekarar 2011

Ya taimakawa Nigeria lashe kofin nahiyar Africa a shekara ta 2013

Shima kyaftin din Nigeria, Joseph Yobo ya bayyana ritayarsa daga bugawa Nigeria wasa.

A can baya dai Stephen Keshi ya taba mika takardar yin murabus din sa bayan da Nigeria ta lashe kofin nahiyar Africa, inda ya bayyana rashin samun goyan baya da kuma karramashi. Amma daga bisani ministan harkokin wasanni na lokacin ya shawo kansa ya ci gaba da aiki.

An bada rahoton 'yan wasan Nigeria sun yi bore a lokacin wannan gasa a Brazil a kan batun kudadensu.