Ana zaman dar- dar a Bukuru a jihar Filato

Hakkin mallakar hoto plateau state govt
Image caption Jihar na fama da tashe-tashen hankula na kabilanci da kuma addini

A Nigeria rahotanni daga jihar Filato na cewa ana zaman dar-dar a garin Bukuru, sakamakon rusa shaguna fiye da 1000 da hukumomin jihar suka yi a daren ranar Litinin.

Dubban 'yan kasuwa da lamarin ya shafa dai na cewa gwamnatin ba ta sanar da su cewa za ta yi aikin rusa shagunan ba.

Haka kuma 'yan kasuwan sun yi zargin cewa gwamnati ba ta ba su dama sun kwashe hajojinsu ba kafin ta rusa shagunan ba.

Sai dai gwamnatin jihar ta ce, ta sanar da 'yan kasuwar shirin rusa shagunan kuma ta ce za ta ma ci gaba da aikin rusau din da zai hada har da gidajen jama'a domin abin da ta kira ayyukan raya kasa.

Karin bayani