Ma'aikatu sun hana yin Azumi a China

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Musulmin yankin sun ce danniyar da ake nuna musu ta fuskar addini da al'adu ne ke janyo karin rikice-rikice

Wasu ma'aikatun gwamnati a China da ke yankin Xinjiang na yammacin kasar, sun hana Musulmi yin azumi a wannan watan na Ramadan.

Wadanda aka hana yin azumin galibinsu malaman makaranta ne da dalibai da kuma ma'aikatan gwamnati wadanda 'yan kabilar Uighur ne marasa rinjaye.

Wata kungiyar 'yan kabilar ta Uighur ta ce wasu ma'aikartun suna bada abincin rana a kyauta.

Galibin 'yan kabilar Uighur sun ce suna addinninsu da al'adarsu na fuskatar barazana daga shugabannin kasar.

Hakan na faruwa yayin da hukumomi ke ci gaba da daukar tsauraran matakan tsaro a wannan yankin mai fama da munanan hare-hare.