Waye Sarki Muhammadu Sanusi II ?

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mai martaba, Sarkin Muhammadu Sanusi na biyu

A irin wasikun da muke samu daga 'yan jaridun nahiyar Afirka, Mannir Dan Ali ya yi nazari kan ko sabon Sarkin Kano zai zama mai iya kawo sauyi kamar yadda ya yi a lokacin yana Gwamnan Babban Bankin Nigeria watau CBN.

Sanusi Lamido Sanusi wanda ya jawo cece-kuce lokacin yana gwamnan CBN, ya samu nasarar cimma burinsa na rayuwa.

Al'umma da dama sun yi matukar mamaki ganin yadda aka zabe shi a matsayin sarkin Kano, saboda girman matsayin a tsakanin Musulmi Hausa-Fulani, maimakon babban dan margayi sarkin Kano, Lamido Ado Bayero.

Dama Malam Sanusi bai taba boye anniyarsa ba ta son zama Sarki a birni mai dimbin tarihi da kyaun gani a Afirka ta yamma.

'Canjin Zamani'

Kakansa, Muhammad Sanusi ya yi mulkin Kano har lokacin da aka tunbuke shi a 1963.

Yanzu sabon sarkin ana kiransa da Muhammed Sanusi II abinda ke bayyana shi a matsayin magaji.

Image caption Gwamnonin arewacin Nigeria sun taya sabon sarki murna

A tsakiyar shekarar 1990, Malam Sanusi Lamido ya ajiye aikin da yake a banki inda ya ke karbar albashi mai tsoka ya tafi kasar Sudan domin neman ilmin Qur'ani da wasu bangarori na addinin musulunci.

Amma sabon sarkin bai taba boye ra'ayinsa na yin muhawara ba saboda haka a karshen mulkin soji cikin shekarar 1999, ya kalubalanci dabbaka shari'ar musulunci a wasu jihohin arewacin Najeriya.

Ya kuma bayyana ra'ayinsa a wata jarida inda ya ce akwai wasu matsaloli da a ganinsa ya kamata a magance su.

'Cece-kuce kan Shari'a'

Kalubalantar shari'a da ya yi ya jawo bambamcin ra'ayi tsakanin sa da malamai masu tsatstsauran ra'ayi a arewacin Nigeria.

Wasu masu dauke da makamai sun yi yunkurin hallaka Marigayi Sarki, Alhaji Ado Bayero wanda ya rasu a watan Yuni yana da shekara 83 bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Yanzu haka dai mutane na sa ido don ganin matakin da sabon sarkin zai dauka kan batun ta'addanci.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dubban magoya bayan sabon Sarkin

Wata matsala da sabon sarkin mai shekaru 53 ke fuskanta ita ce ta bayyana ra'ayinsa sakamakon rawanin da ya rufe masa baki.

Hakazalika, sabon sarkin ya fara yin huduba a Sallar Juma'a da ake yi mako-mako a babban masallacin cikin garin Kano sabanin wanda ya gaji sarautar daga hannunsa wanda yin hakan watakila wata hanya ce ta bayyana manufofinsa.

Sabon sarkin wanda baya jin tsoro, ana sa ran zai yi amfani da matsayinsa wajen magance matsalar hare-haren kungiyar Boko Haram, rashin aikin yi da rashin saka yara a makaranta, ta hanyar samar da daidaito a tsakanin 'yan siyasa da sauran talakawa wadanda a koda yaushe su ke zargin manufofin gwamnati.

Jonathan ya ki taya shi murna

Jam'iyyar PDP mai mulkin Nigeria ta yi riga malan masallaci inda ta yi gaggawar bayyana wani wanda za a nada a sarautar Kano kafin daga bisani Gwamnan Jihar, Rabiu Musa Kwankwaso ya sanar da nasa zabin.

Kawo yanzu Shugaban kasa, Goodluck Jonathan wanda ya dakatar da sabon sarkin daga shugabancin Babban bankin Nigeria bai taya shi murna ba.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mr Jonathan yana yawan ziyartar tsohon Sarkin Kano.

Tsohon Gwamnan Babban Bankin-CBN din ya fallasa batun badakalar kudi dala biliyan 20 da suka yi layar zana a kamfanin mai na kasa.

Sai dai alamu na nuni da cewa matukar sabon sarkin na son tafiya tare da gwamnati to lallai sai ya janye wannan mataki nasa.

Amma kamar yadda ake harsashen cewa ba bu wani dan siyasa da zai fito takarar shugabancin kasa ba tare da neman kuri'ar al'ummar jihar Kano ba, a don haka watakila dole Mr. Jonathan ya cire hularsa tare da ajiye gwiwarsa a fadar ta kano don girmama al'adunsu kafin samun kuri'arsu.

Wane ne Sarki Muhammadu Sanusi II?

  • An haife shi a zuriyar sarakunan fulani a ranar 31 ga watan Yuli 1961.
  • Jika ne ga sarki Sanusi da aka sauke daga gadon sarauta.
  • Ya samu digiri a fannin tsimi da tanadi da fannin addini Musulunci.
  • An nada shi mukamin gwamnan Babban Bankin Nigeria (CBN) a watan Yuni 2009.
  • Mujallar Banker ta bayyana shi a matsayin gwarzon shekara a 2010.
  • An dakatar da shi a watan Fabrairu bayan sun samu sabani da shugaban kasa.
  • An kuma nada shi a matsayin Sarkin Kano ranar 8 ga watan Yuni 2014.
  • Sunansa ya canja daga Sanusi Lamido Sanusi zuwa Muhammad Sanusi II.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yana tsage gaskiya komai dacin ta