Amurka ta soki kisan dan Palasdinu

Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Lamarin ya kawo tashin hankali a yankunan Palasdinawa

Amurka ta yi tir da kashe wani saurayi Bafalasdine, wanda aka sace a gabacin birnin Qudus.

Amurkan ta kuma bayyana kisan a matsayin mummunan kisan kai.

Fadar Shugaban Amurka ta White House ta ce tana sa ido sosai game da bincike kan mutuwar Mohammed Abu Khdair din mai shekaru 17.

Ta kuma bukaci 'yan Isra'ila da Palasdinawa da su hana halayyar ramuwar gayya.

Pirayim Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana kisan a matsayin wani abun kyama.

Kisan dai ya zo ne kwana daya bayan jana'izar matasan Isra'ila 3 da aka kashe wadanda aka gano gawarsu a gabar yamma ta kogin Jordan.