Kaciya: Maza 19 sun mutu a Afrika ta Kudu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sai dai ba kowa ne a kasar ke yin kaciyar ba

Ma'aikatar lafiya ta Afrika ta Kudu ta ce wasu maza 19 sun mutu, a lokacin da aka yi kokarin yi musu kaciya.

Haka kuma an kwantar da wasu mazan 50 a asibiti, saboda karancin ruwa a jikinsu da kuma wasu cututtukan da suka kamu da su.

Gwamnatin kasar ta bukaci shugabannin gargajiya da su yi aiki tare da kwararrun likitoci maimakon baragurbin masu fida domin guje wa asarar rayuka da kuma samun raunuka a lokacin yin kaciyar.

A al'adance a Afrika ta Kudu ana kebe mazan da za a yi wa kaciya na wasu kwanaki, inda ake wasu tsubbace-tsubbace wajen yi musu kaciyar.