An kai karar hukumar leken asirin Birtaniya

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption GCHQ ta tabbatar da cewa tana gudanar da aikin ta bisa doka

Wasu kamfanonin bakwai dake samar da hanyoyin sadarwa na Intanet sun kai karar hukumar leken asirin Birtaniya wato GCHQ

Kamfanonin wadanda suka fito daga Kasashen Amurka da Birtaniya da Netherlands da kuma Korea ta Kudu sun hade da wasu masu fafutukar kare sirri na kasashen duniya domin kai hukumar kara bisa zargin kaiwa kayayyakin aikinsu na samar da hanyar Intanet hari.

Wannan dai shine karo na farko da hukumar ta GCHQ ta Birtaniya ta fuskanci irin wannan mataki da aka dauka akanta

Wannan mataki ya biyo bayan zarge zarge game da yadda gwamnati take satar leken asiri da tsohon jami'in leken asirin Amurkan nan Edward Snowden ya yi Kamfanonin suka ce abinda hukumar ta GCHQ ta yi musu ya saba ka'ida

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption GCHQ ta tabbatar da cewa tana gudanar da aikin ta bisa doka

Kamfanonin sun yi zargin cewa hukumar GCHQ ta yi amfani da wasu hanyoyi wajen tatsar bayanai na sirri daga wajensu

Kamfanonin da suka dau wannan mataki na kai koke sun hada da GreenNet dake Birtaniya da Riseup a Amurka da Greenhost dake Netherlands da Mango a Zimbabwe da Jinbonet a Korea ta Kudu da kuma Chaos Computer Club dake kasar Jamus.

Sai dai hukumar ta GCHQ ta tabbatar da cewa tana gudanar da aikin ta bisa doka