Bukatar kafa sansanin 'yan gudun hijira a Borno

Hakkin mallakar hoto NEMA
Image caption Dubun dubatar mutane ne suka tsere daga gidajen su a Borno

Wani dan majalisar dokoki ta kasa daga yankin Borno ya yi kira ga gwamnati da ta kafa tsayayyen sansani na 'yan gudun hijira a jihar Borno

Hakan na zuwa ne yayinda mutanen da tashe-tashen hankulan da ake yi a jihar Borno suka kora daga gidajensu ke kukan halin kunci na rayuwa.

Dan Majalisar Abdur Rahman Terab mai wakiltar yankin Bama wanda ya gabatar da kuduri a gaban majalisar dokokin Najeriyar a ranar Laraba, ya shaidawa BBC cewa ya kamata a samu wurin da za'a tsugunar da duk wadanda rikici ya sa suka bar gidajen su.

Dubun dubatar mutane ne suka tsere daga gidajen su sakamakon hare haren da 'yan bindigar da ake zargin 'yan Boko Haram ne suke kaiwa a sassan jahar Borno.