Kwanaki 80 da sace 'yan matan Chibok

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar Boko Haram wadda ta sace 'yan matan ta ce zata sayar da su ne.

A ranar Alhamis ne aka cika kwanaki 80 cif tun bayan da aka sace 'yan mata fiye da 200 daga wata makarantar sakandaren kwana da ke garin Chibok a Jihar Borno ta arewa-maso-gabascin Najeriya.

Haka kuma kusan wata guda ke nan tun bayan da babban hafsan tsaron Najeriyar, Air Chief Marshal Alex Badeh, ya ce sojojin kasar sun san inda 'yan matan suke, amma kuma suna taka-tsan-tsan don gudun aikata wani abu da ka iya jefa rayuwar 'yan matan cikin hadari.

Sai dai kuma masu fafutukar neman a sako 'yan matan na ci gaba da kira da ga hukumomin da su yi duk mai- yiwuwa don ganin an mayar da su ga iyayensu.

''Abin da ke damunmu shi ne wadannan kashe-kashe da sace 'yan mata sai dada karuwa su ke yi suna kuma bazuwa,'' inji Dokta Jibrin Ibrahim jigo a kungiyar BringBackOurGirls.

Karin bayani