Iyayen 'yan Chibok sun fara yanke kauna

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kasashen Amurka da Burtaniya da Faransa da Isra'ila da China na daga cikin kasashen da ke taimaka wa Najeriya

Wasu iyayen 'yan matan Chibok sun ce sun fara cire tsammanin sake ganin 'ya'yansu ganin yadda aikin cetonsu ke tafiyar hawainiya.

Iyayen sun ce a yanzu suna cikin bakin ciki da alhinin ganin cewa an cika kwanaki 80 ba tare da gwamnati ta ceto 'ya'yansu daga hannun Boko Haram ba.

Kungiyoyi a ciki da wajen Najeriya na ci gaba da yin gangamin matsa wa gwamnatin Najeriyar lamba, domin daukar matakin ceto 'yan matan, amma har yanzu babu amo ba labari.

Sai dai gwamnatin Najeriyar ta sha nanata cewa tana iya bakin kokarinta don ganin an ceto dalibai matan fiye da 200.

A baya dai bayanai sun nuna cewa, an yi kokarin musayar 'yan matan da wasu mayakan kungiyar Boko Haram, sai dai daga bisani aka fasa.