Gaza: Harin Isra'ila ya raunata mutane 10

Image caption Rokoki 20 ne Hamas ta harba zuwa cikin Isra'ila da zirin na Gaza.

Akalla Falasdinawa goma ne suka samu raunukka a wani hari ta sama da Isra'ila ta kai kan zirin Gaza da sanyin safiyar ranar Alhamis.

Isra'ilar dai ta ce harin mai da martani ne ga wasu hare-haren roka da aka kai mata daga yankin.

Wani jami'in lafiya na Falasdinawa a zirin na Gaza Ashraf Alkidrah, ya ce duka mutane goman da suka samu raunukka fararen hulla ne kuma uku daga cikinsu mata ne.

Hare-haren sun zo ne bayan makamin roka da aka harba daga Gaza ya fada kan wani gida a garin Sderot na Israila da sanyin safiyar Alhamis, inda ya lalata gidan sosai da kuma wani titi da ke kusa da shi; tare katse wutar lantarki abin da ya jefa daukacin garin a cikin duhu.

Karin bayani