Na'ura mai hana yara shiga shafin intanet

Image caption Yara kan iya samun kudin sayen tikitin shiga internet bayan gama aikace-aikacen gida

Ana hada wata na'ura da ba ta barin yara shiga shafin intanet har sai sun gama aikin gida a kasar Amurka.

Na'urar mai suna Kudoso za ba ta iyaye damar jera wa yara aikace-aikacen gida da za su yi kafin ta ba su damar bude shafin na intanet.

Wadanda suka kera na'urar na fatan daga karshe su saka manhajar duba lafiyar jiki a ciki domin amfanin yaran da ke motsa jiki kodayaushe.

Wata kwararriya kan yadda iyaye ke zama da yaransu ta shaida wa BBC cewa tana ganin wannan fasahar da dan yi tsauri.

Marubuciyar kan zamantakewar iyaye da 'ya'yansu Judy Reith ta ce ana samun karuwar nuna damuwa game da amfani da intanet (ga yara.)

''Na gana da iyaye da yawa kuma damuwarsu ta farko ita ce ababen da ci gaba kimiyya ya kawo, wannan kuma ba zai gushe nan kusa ba,'' inji ta.

Image caption Yaro kan samu maki kan kowane aiki daya da ya gama.

Sai dai ta ce ''maganar iyaye tana da karfin tasiri sosai ko da kuwa iyayen ba su jin hakan; don haka kamata ya yi su kafa wasu dokoki amma ba masu tsauri ba kan kowane abu ciki har amfani da intanet''

Mrs Reith ta kara da cewa kamar yadda ya ke da muhimmanci iyaye su rika sa ido kan shafukan da yaransu ke shiga a intanet, haka ya ke muhimmanci su ma kansu su san irin shafukan da za su rika shiga''

Wanda ke kokari hada na'urar Rob Irizarry na kokarin ganin ya samu kudaden da zai dauki nauyi aikin samar da na'urar ta wata gidauniya, wanda ake kan yi tun watanni 18 da suka wuce.

''A yau iyaye na cikin halin tsaka-mai-wuya game da yadda za su kayyade yawan lokacin da yaransu za su kwashe kan intanet da kuma irin shafukan da suka ziyarta; inji shafinsa na intanet mai suna kickstarter.

Karin bayani