Wata tayi cacar dalar Amurka miliyan 3 a rana guda

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Caca ta zamewa wasu tamkar jaraba

Wata mata da caca ta zame ma ta jaraba ta shigar da karar gidan cacar nan na Ritz dake nan London, bayan da ta yi asasar kusan dala miliyan 3 da rabi a dare daya.

Nora Al Daher, wadda mijinta babban kusa ne a ma'aikatar harkokin wajen daular Oman, ta ce ta shigar da karar ce saboda ma'aikatan gidan cacar na Ritz sun yi amfani da yadda cacar ta zame ma ta jaraba wajen lashe kudin na ta.

Ta fadawa wata kotu a nan London cewa kamata ya yi ma'aikatan su hana ta cigaba da cacar, amma sai su kyaleta ta cigaba.

Sai dai gidan cacar na Ritz ya musanta wannan zargi.

Wannan batu dai ya je gaban kotu ne bayan gidan cacar ya yi kara Nora Al Daher saboda rashin biyan ragowar kudi fiye da dalar Amurka miliyan guda.