Samsung zai daina talabijin din plasma

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yanzu mutane sun fi son talabijin ta ado mai wata siffa ta daban'

Kamfanin kayan laturoni na Samsung zai daina kera talabijin mai allon plasma inda zai mayar da hankalinsa kan kera talabijin ta UHD.

Kamfanin na Korea ya ce nan da zuwa ranar 30 ga watan Nuwamba zai daina kera talabijin din, saboda rashin kasuwarta.

A maimakonta zai mayar da hankalinsa kan abin da jama'a suka fi bukata wato talabijin mai fasahar UHD.

Kamfanin ya kara da cewa, burinsa shi ne ya samar wa jama'a abin da zai fi biya musu bukata.

Daman a shekarun nan kamfanonin Panasonic da Sony da Hitachi da kuma Pioneer sun daina kera talabijin din mai plasma.

Shi ma kamfanin LG ana sa ran zai bi sahun takwarorin nasa.

Hakkin mallakar hoto Getty

Shi dai talabijin mai kirar plasma, ana sha'awarsa saboda haske, da duhun launi da kuma babbar fuska, wanda hakan yasa aka fi sson sa wajen kallon wasanni da fim.

Sai dai kuma, yana bukatar wutar lantarki sosai, kuma yana da girma fiye da wadanda aka fi so yanzu, samfurin LCD da LED.

Editan mujullar TrustedReviews, Evan Kypreos ya ce,ba abin mamaki ba ne yadda kamfanin Samsung ya dauki wannan mataki.