An gano shirin Birtania a Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Frai ministan Birtaniya David Cameron

Wasu bayanai sun bayyana wani tsattsauran shiri da hukumar sojin Birtaniya ta yi, shekaru biyu da suka gabata na shiga rikicin Syria, abin da ya kunshi ba da horo ga dubban 'yan tawayen Syrian.

Tsohon babban hafsan sojin Birtaniyan, David Richards, shi ne ya tsara shirin, wanda a cikinsa ya bayar da shawarar cewa, kasashen yammacin duniya, na da zabi.

Zabin shi ne ko dai su zauna kada su dauki wani mataki, su bari Shugaba Assad, ya yi nasara, ko kuma su ba da isasshen horo da kuma kayan aiki ga dubban 'yan tawaye domin kawar da shugaban.

Frai ministan Birtaniya, David Cameron da manyan hafsoshin sojin Amurka ne suka nazarci shirin, amma suka yi watsi da shi a kan cewa ya yi tsauri da yawa.