Borno: Wasu matan da aka sace sun tsere

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Har yanzu ba a san inda 'yan matan Chibok suke ba

Rahotanni daga Jihar Borno ta arewa maso gabashin Nigeria sun ce wadansu daga cikin matan da aka sace daga yankin Askira Uba makonni biyu da suka wuce sun kubuta daga hannun wadanda suka sace su.

Mazauna yankin sun shaida wa BBC matan da suka kubuta su uku ne, kuma yanzu haka suna asibiti suna karbar magani.

Daya daga cikin matan ta ce masu tsaronsu suna barci suka haura katanga suka tsere daga inda ake tsare da su.

Babu wanda ya dauki alhakin sace matan, amma ana zargin mayakan kungiyar Boko Haram ne suka yi awon gaba da su.

Har yanzu dai ba a san inda 'yan mata fiye da 200 wadand aka sace daga makarantar sakandiren Chibok suke ba, fiye da kwanakin 80 tun bayan yin awon gaba da su.