Yakar Ebola: Ana bukatar dala miliyan 10

Likitoci masu kula da wadanda ke fama da cutar Ebola Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu daga cikin kasashen da abin ya shafa sun ce suna bukatar karin ma'aikatan lafiya

Hukumar Lafiya ta Duniya, wato WHO, ta ce ana bukatar wasu makudan kudi don tunkarar cutar Ebola a yankin yammacin Afirka.

Daraktan hukumar ta WHO mai kula da nahiyar Afirka, Dokta Luis Gomes Sambo, ya fadi hakan a karshen taron da ministocin lafiya na kasashen Afirka 11 suka kammala ranar Alhamis a Accra, babban birnin kasar Ghana.

"Mun kiyasta cewa ana bukatar dala miliyan goma nan take don tunkarar wannan matsala a watanni shida masu zuwa", inji Dokta Sambo.

Jami'in na WHO ya kuma bayyana cewa ministocin kasashen Afirka sun kawo shawarar kafa wani asusun kula da lafiyar al'umma cikin gaggawa.

"Taron shugabannin kasashen nahiyar ya amince da wannan shawara; kuma ko da yake kudin da aka samu bai taka kara ya karya ba, tuni muka fara amfani da abin da ke asusun don tallafawa kasashen da abin ya shafa", inji shi.

Zuwa yanzu dai cutar ta Ebola ta haddasa mutuwar mutane fiye da 450 a kasashen Guinea, da Saliyo, da Liberia.

Karin bayani