An gabatar da korafi kan Facebook

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A kan binciken Facebook ya ce ya dauki matakan kare bayanan masu amfani da shafin

Masu rajin kare sirrin masu amfani da shafin sada zumunta da muhawara na Facebook sun bukaci da hukumomi su duba shirin shafin na nazarin yanayin kwanciyar hankalin masu amfani da shi.

Masu rajin sun gabatar da bukatar ne ga Hukumar sanya ido kan harkokin kasuwanci ta Amurka.

Korafin ya shafi shirin Facebook na sarrafa yanayin kwanciyar hankalin masu amfani da shafin.

Facebook ya gudanar da bincike ne a 2012 a kan ma'abota shafin kusan 700,000 ta hanyar sauya sakonnin da ake aika musu ta shafin.

Facebook ya yi binciken ne da hadin guiwar wasu jami'oin Amurka biyu.

Hakkin mallakar hoto AFP

A nazarin yana duba ko sauya sakonnin da ake tura wa mutane ta shafin na wani labari da ya shafi rayuwarsu ko sabunta labarin, zai iya sauya yanayin kwanciyar hankalinsu.

Wadanda suka gabatar da karar dai suna korafin cewa Facebook ya saba ka'idar aiki da ta shafi amfani da mutane wajen gudanar da gwaji.

Masu rajin sun ce bisa tsarin binciken da niyya kamfanin na Facebook ya yi wasa da hankalin mutane.

Kuma ya yi hakan ne ba tare da izinin masu amfani da shafin ba kafin gudanar da binciken.

Kwamishinan yada labarai na Birtaniya shi ma yana gudanar da bincike ko Facebook ya saba dokokin kare bayanan jama'a a lokacin binciken.